IQNA

Yunkurin Sace Wani Kwafin Kur’ani Ya Ci Tura

23:39 - October 23, 2016
Lambar Labari: 3480876
Bangaren kasa da kasa, hukumar kula da ayyukan bude ido a Masar ta sanar da kame wani ma’aikaci da ya sace wani kwafin kur’ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa nwannan kwafin kur’ani da Yaum Sabi cewa, jami’an yan sanda sun kame wannan mutum ne a lokacin da yake shirin sayar da sace.

Mutumin dan shekaru 53 dan kasar Masar ne da yafito daga garin Faisal a cikin gundumar Jizah, kuma yana da nufin sayar da wannan kwafin kur’ani ne mallakin hukumar kula da ayyukan yawon bude ido ta kasar, a kan kudi dalar Amurka miliyan guda da dubu 200.

Jami’an ‘yan sanda sun kasance suna bibiyar wannan mutum, inda suka rutsa da shi a cikin gidansa, kuma suka samu wannan kwafin kur’ani ajiye a cikin gidansa, a tar kayan tarihi mallakin kan haka an kama shi da laifin satar kayan tarihi mallakin gwamnatin kasar.

3539965


Yunkurin Sace Wani Kwafin Kur’ani Ya Ci Tura

Yunkurin Sace Wani Kwafin Kur’ani Ya Ci Tura

Yunkurin Sace Wani Kwafin Kur’ani Ya Ci Tura

captcha