Bangaren kasa da kasa, wani malamin jami'ar Mikane Yesus ta kasar Ethiopia ya bukaci da a gudanar da wani shiri na bayar da horo kan sanin addinin muslunci da kur'ani a jami'oin kasar.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren hula da jama'a na cibiyar yada al'adun muslunci cewa, Sayyid Hassan Haidari shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a Rthiopia ya gana da Marsha Mingiste, shugaban bangaren hula tsakanin addinin kiristanci da muslunci na jami'ar Mikane Yesus.
Wanan ganawa da ta gudana tsakanin jami'in na diflomasiyar kasar Iran da kuma shugaban bangaren kula da harkokin addinai na kiristanci da msulunci a wannan jami'a ta Mikane Yesus, ta zo ne adaidai lokacin da dukkanin bangarorin suke bukatar samun hadin kai a tsakanin al'ummomin biyu.
Kasar Ethiopia dai kasa ce wadda ta shahara a duniya wajen tsohon tarihinta, da kuma irin rawar da al'ummarta ta taka wajen karbar addinin kiristanci da yada atsakanin al'ummomi tun kafin zuwan muslunci.
Haka nan kuma al'ummar Ethiopia ta kasance a sahun gaba wajen karbar musulmi da suka yi gudun hijira a farkon bayyanar addinin muslunci a hannun annbin rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
Marsha Mingiste shi ne shugaban bangaren kula da harkokin addinai na kiristance da muslucni a wannan jami'a, da kuma sanin haniyoyin da za a kara karfafa alaka a tsakanin mabiya addinan biyu, ya kuma bayyana cewa a shirye su aiwata da wannan shiri tare da Iran da kuma bangarensa.
A nasa bangaren karamin jakadan ya bayyana cewa,a shirye suke su hada kai da wannan jami'oin kasar Ethiopia musamman ma wannan jami'a ta Mikane Yesus, wadda ta kasance daya daga cikin muhimman jami'oi a kasar, domin ganin an kara inganta masaniya kan addinin muslunci musamman a tsakanin mabiya addinin kirista, domin kara samun fahimtar juna da zaman lafiya mai dorewa.
http://iqna.ir/fa/news/3540927