Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na hafington post cewa, Tana Ilah wata yarinya ce musulma wadda take da matukar sha'awar samun hotuna na wurae masu ban mamaki.
Kasantuwarta musulma ta yi amfani da wanann damar a duk lokacin da ta ga wani yana salla a wani wuri da ya bata sha'awa sai ta dauki hotonsa, kamar yadda kuma ta rika tara wadannan hotuna ta hanyar yanar gizo.
Ta bayyana cewa a karon farko da ta taba ganin dusar kankara shi ne lokacin da ta yi tafiya zuwa kasar Canada, inda ta ga musulmi suna salla a cikin dusar kankara, wanda hakan ya bata sha'awa matuka, inda ta dauki hotunasu.
A halin yanzu dai wannan yarinya ta tara hotuna masu tarin yawa na mutane daban-daban a wurae masu ban mamaki da ake yi salla, inda take sakawa a cikin shafin na Instegram.
http://iqna.ir/fa/news/3540619