Mahalarta wannan taro dai suna mayar da hanakali domin samo hanyoyin bunkasa harkokin hada-hadar bankuna da kuma saka hannyaen jari a cikin bankunan nahiyar Afirka, kamar yadda kuma shi ma bankin muslunci yake daya daga cikin bankuna da suke taka rawa a wannan fuska.
A kan haka a wannan zaman taro ne za a samar da hanyoyi na bunka harkokin bankuna da kuma yadda za a rika tsara musayar kudade a tsakanin bankuna da kuma sauran takwarorinsu an kasashen duniya, da zimmar habbaka tattalin arzikin nahiyar Afirka.