IQNA

21:29 - November 04, 2016
Lambar Labari: 3480908
Bangaren kasa da kasa, Kwamitin masallacin birnin York na kasar Birtania, ya fara gudanar da wani shiri na tattara taimakon madara ta gari ga miliyoyin kananan yara da ke fama da matsalar yunwa a kasar Yemen, sakamakon hare-haren da Saudiyya ke kaddamarwa a kasar.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a cikin wani bayani da kwamitin masallacin ya fitar wanda shafin yada labarai na minsterfm ya watsa, ya bayyana cewa yana kira ga dukkanin musulmi da ma wadanda ba musulmi ba da suke son su taimaka kananan yara a Yemen, da su bayar da gwangwanin madara ta gari akall guda daya, ko kuma su bayar da kudin saye, domin aikewa ga kananan yara da ke cikin halin rai kwakwai mutu kwai a kasar Yemen, sakamakon hare-haren da Saudiyya ke jagoranta kan al'ummar wannan kasa tsawon kusan shekaru biyu a jere.

Wannan mataki dai ya zo ne sakamakon sanarwar da asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya bayar ne, a kan cewa sakamakon hare-haren da ake kadsdamarwa kan al'ummar Yemen kusan shekaru biyu a jere da kuma killace da su da aka yi da hana shigar da komai na abinci a kasar, miliyoyin yara suna fuskantar matsalar rashina binci, inda wasunsu suke mutuwa sakamaon hakan.

Rahotannin da majalisar dinkin duniya ta bayar a farkon shekarar nan sun nuna cewa hare-haren saudiyya a Yemen sun yi sanadiyyar mutuwar kanann yara fiye da dari takwas, wanda hakan ya sa aka saka kasar a cikin jerin sunayen kasashe masu kashe yara, amma daga bisani babban sakataren majalisar dinkin duniya ya sanar da cire sunanta, sakamakon abin da ya kira barazanar da aka yi masa.


3543137


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، IQNA ، Birtania ، York ، yemen ، UNICEF
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: