IQNA

20:30 - November 06, 2016
Lambar Labari: 3480913
Bangaren kasa da kasa, a yau ne aka fara gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki ta daliban jami'a a birnin Alkahira na kasar Masar.
Gasar Hardar Kur'ani Mai Tsarki Ta Daliban Jami'a A Birnin Alkahira
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwahdah cewa, bababr cibiyar kula da harkokin al'adun musulunci ta daliban jami'oi ce ta dauki nauyin shirya wannan gasa.

Daliban jami'ar Alkahira ne zalla su ke gudanar da wannan gasa, inda sauran rassan jami'ar daga koina cikin fadin kasar Masar suka iso domin halartar wannan babbar gasa ta hardar kur'ani mai tsarki.

Gasar dai ta shafi bangarori daban-daban, da hakan ya hada da bangaren hardar izihi 20, sai kuma izihi 15, da kuma izihi 10 da kuma izihi 5, gwargwadon abin da dalibi ya ga zai iya yi ba tare da takura ba.

Baya ga hardar kur'ani mai tsarki kuma, akwai bangarori da suka shafi ilmomin karatun kur'ani da hukunci da wasu lamurra da suka danganci addini, wadanda za su zoa cikin tambayoyi da za ayi wa daibi.

Akwai wakilan cibiyoyin addini da dama da suka halarci wurina matsayin 'yan kallo, wadanda suke kara karfafa gwiwar dalibai kan lamarin kur'ani mai tsarki.

3543841


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، IQNA ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: