IQNA

23:55 - November 15, 2016
Lambar Labari: 3480943
Bangaren kasa da kasa, wata kotu a kasar Sudan ta yanke hukuncin daurin shekara guda a gidan kaso da bulala 40 a kan wani barawon kur’ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alwahdah cewa, kotun Alhaj Yusuf karkashin alkali Hassan Sayyid Hussaina yankin Mansirah da ke birnin kahrtum, ta yanke hukuncin daurin shekara guda da bulala 40 a kan barawon kur’ani.

Mutumin da ya sace kur’anin an kame shi ne bayan da wani mutum ya sanatr da ‘yan sanda abin da ya faru, a lokacin da wannan mutum ya dauki kur’anin daga cikin masallaci, bayan kame shi kuma ya amsa laifinsa.

Haka nan kuma na kame mtumin da ya sayi kur’anin daga hannun barawon, wanda ya sheda ma jami’an tsaro cewa shi ne ya sayi kur’anin, amma bai san cewa na sata ne ba.

Kotu ta yanke hukunci a kan mutumin da yay i satar na daurin shekara guda a gidan kaso, mai sayen kuma ya dauki alkawalin cewa ba zai sake sayen abin sata ba.

Kasar Sudan na daga cikin kasashen yankin da ake samun dadaddun kur’anai bugun hannu wadanda suke da kima idan za a sayar da su.

3546143


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: