IQNA

19:35 - November 17, 2016
2
Lambar Labari: 3480948
Bangaren kasa da kasa, mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah mazauna biranan Birmingham da Landan Luton sun yi tattaki a birnin Bradford.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Asian Image cewa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzo (SAW) sun yi tattaki a birnin Bradford na kasar Birtaniya domin tunawa da arbain na shahadar Imam Hussain (AS).

Ali Shah daya daga cikin mahalarta wannan gangami da tattaki ya sheda ma manema labarai cewa, sun fito domin su nana damuwarsu da alhininsu dangane da abin da ya samu jikan manzon Allah (SAW) Imam Hussain (AS).

Ya ce wannan lamarti yana da matukar muhimmanci a gare su, domin hakan yana a matsayin taya manzon manzon Allah da iyalan gidansa bakin cikin abin da ya faru da su ne na zalunci da kisan gillar da aka yi kansu.

‘Yan sandan gwamnatin Birtaniya sun kasance tare da masu tattakin, domin ba su kariya, da kuma tabbatar da cewa wasu ba su kawo musu matsala ko rashin tsari a tattakin nasu ba.

3546600


Wanda Aka Watsa: 2
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Abdul
0
0
free zakzaky insha allah
Abdul
0
0
free zakzaky insha allah
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: