IQNA

Harin Bam Ya Kashe Mutane fiye Da 70 A Iraki

21:51 - November 24, 2016
Lambar Labari: 3480970
Bangaren kasa da kasa, wani harin bam da aka kai kan masu ziyara a Iraki ya kasha mutane kimanin 80 akasarinsu kuma mutanen Iran ne.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar alalam cewa, kamfanin dillancin labaran Reuters ya bada rahoton cewa, wata babbar mota makare da boma bomai ta yi bindiga a garin hilla na kasar Iraqi ta kuma yi sanadiyyar kisan mutane akalla 80 mafi yawansu Iraniyawa wadanda suke kan hanyarsu ta komawa gida bayan makokin arba'en a ranar litinin da ta gataba.

An kai harin ta'addancin ne a garin Hilla wanda ke kilomita dari daga kudancin birnin Bagdaza, kuma tuni kungiyar Daesh ta dauki alhain kai harin a wani sakon da ta aike a cikin yanar gizo.

Majiyar asbitoci da na yansanda sun bayyana cewa mutocin masu ziyarar arba'in guda biyar ne harin kunan bakin waken ya shafa. Labarin ya kara da cewa mutanen sun tsaya a wurin ne don cin abinci a cikin wani dakin cin abinci kusa da wurin kafin bom din ya tashi.

Wannan dai shi ne hari na farko mafi muni wanda kungiyar daesh ta kaiwa musulman shia wadanda take daukarsu kafirai, wadanda kuma suka yi ruwa da tsaki wajen yakar Kungiyar a tungarsu ta karshe a birnin Musil na kasar Iraqi daga ranar sha bakwai ga watan da ya gabata.

3548617


captcha