Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna
ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafaqana cewa,
Ilham Umar wata musulma 'yar asalin kasar Somalia da ta lashe zaben kujerar
majalisar dokoki a jahar Minnesota, ta bayyan acewa wani direba da ya dauke ta
zuwa Washington ya yi barazanar kasheta har lahira.
Umar ta rubuta a shafinta na yanar gizo na Facebook cewa, direban ya bayyana ta a matsayin 'yar ta'adda ta kungiyar daesh, yana mai yi mata barazana da cewa zai iya halaka ta.
Tun bayan da aka zabi Trump a matsayin shugaban kasar Amurka, kyamar musulmi da kuma yi musu barazana kan rayuwarsu ke ci gaba da karuwa a dukkanin yankunan kasar, inda musulmia halin yanzu ke rayuwa cikin halin rashin tabbasa a Amurka.