Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya
habarta cewa, ya nakalto daga Shafin yada labarai na jaridar
Tottenham Post ya bayar da rahoton cewa, a yau daruruwan musulmi mazauna birnin
sun gudanar da jerin gwano cikin lumana, domin nuna murnarsu da zagayowar
maulidin manzon Allah (SAW).
Rahoton ya ce musulmin sun rika daga kyallaye masu launin kore da fari, domin nuna sakon zaman lafiya irin na addinin muslunci ga sauran dukkanin al'ummomi.
Nadim Amin daya ne daga cikin wadanda suka shirya gudanar da wadannan taruka a kasar Birtaniya, ya bayyana cewa suna shirya tarukan maulidin manzon Allah (SAW) a kowace shekara, a wannan shekara suna yin amfani da wannan damar domin kara wayar da kan jama'a wadanda ba musulmi kan sakon aminci da kaunar juna tsakanin 'yan adam da manzon Allah ya zo da shi.
Ana gudanar da irin wadannan taruka dai a kasashen musulmi da dama, wanda akasari an fara su ne daga yau, yayin da kuma wasu sun fara gudanar da tarukan nasu tun daga lokacin da wannan wata mai albarka ya tsaya.