Moon ya ce ya zama wajibi Isra'ila ta janye daga yankunan Palastinawa da take rike da da su tun daga shekara ta 1967, domin kuwa a cewarsa hakan ya sabawa dukaknin dokokinna kasa da kasa.
Kamar yadda kuma ya bayyana cewa fiye da mutane dubu 600 ne suke cikin mawuyacin hali a yankin an Gaza sakamaon killacewar da Isra'ila take yi wa yankin tsawon shekaru, wanda shi ya saba wa dukkanin kudurori na majalisar dinkin duniya.
Wannan furuci na Ban Ki Moon dai bai zowa kowa da mamaki ba, kasantuwar cewa ya kwashe tsawon shekaru goma a jere yana rike da mukamin babban sakataren majalisar dinkin duniya, amma bai taba furta cewa mamayar yankunan Palastinawa da Ira'ila ke yi ya sabawa kaida da doka ba sai yanzu, da ya rage sauran yan kwanaki da ba su mako biyu ba ya bar ofishin.