Wannan kira ya zo ne sakamakon abubuwan da suke wakana a halin yanzu a wasu birane na kasar ta Birtaniya, inda aka samu wasu kungiyoyin masu kymaar musulmi da suke kai hare-hare kan cibiyoyin musulmi da masallatai, da hakan ya hada har da wasu birane da ke cikin yankin Scotland.
A kwanakin baya ma wata kotun birnin Londan ta daure wasu 'yan kasar ta Birtaniya da suka keta alfarmar wani masallaci a birnin.
Musulmin Birtaniya dai sun bayyana karuwar ayyukan nuna kyama a gare su ne a cikin lokutan baya-bayan nan, tun bayan cin zarafin wasu musulmin da aka yi a birnin Manchester a cikin shekara ta 2015 da ta gabata.