Kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Aljazeera cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Morocco ce ta bullo da wannan shiri, wanda ya kebanci mata da ba su iya karatu da rubutu ba.
Adadin matan da suka shiga cikin shirin dai sun kai dubu 67 a dukkanin fadin kasar, kuma a cikin watanni uku ne suka kammala shirin, inda suka rubuta kalmomi dubu 77 na kur’ani a cikin wannan lokaci.
Wannan shiri dai ya samu gagarumar karbuwa a tsakanin al’ummar kasar ta Morocco musamman ganin cewa akwai mata wadanda ba su taba zuwa makaranta ba, kuma suna da sha’awar ganin sun koyi karatu da rubutu musamman a bangaren addini.
Daya daga cikin waanda suka halarci shirin ta rubuta kur’ani mai tsarki cikakke, kuma ta bayar da shi ga ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar a matsayin kyauta ta musamman ga sarkin kasar Muhammad na shida.
Mahukunta a wannan bangare sun ce za su sakaya sunan matar kamar yadda ta bukaci a yi hakan.