Yace hakika wadanda suke da irin wannan tunani ga alama sanyi ya taba kwakwalensu ne har suka manta da Isra'ila da kuma matsayinta dangane da muslunci.
Tun kafin wannan lokacin da Umar salim ta bata yin wani kira makamancin wannan na neman a kulla alaka takanin Azhar da Isra'ila, wanda hakan ya sanya malamajn Azhar fitar da fatawar barranta da shi.
Mutumin dai ya kwashe tsawon shekaru a kasar Amurka, wanda ake zarginsa da cewa yana daga cikin masu yi ma yahudawa aiki a kasashen muslmi, sakamakon yadda yak efitowa afili yana kare manufofin Isra'ila a duniya.