Daga cikin canjin da aka samu kuwa har da bayar da dama ga mata musulmi da suke aikin gwamnati da suka saka hijabi irin na muslunci ba tare da wata matsala ba.
Wannan mataki ya sanya musulmia jahar ta Califirnia yin godiya ga hukumar 'yan sanda ta jahr, inda mata musulmi a halin yanzu suke da 'yancin zuwa wuraren aikinsu da hijabi ba tare da wani ya ci zarafinsu kan hakan, domin kuwa zai fuskanci fushin hukumar 'yansanda kan hakan.
A kwanakin baya ne dai wani jami'in 'yan sanda yankin Long Beach da ke cikin jahar ya ci zarafin wata mata musulma saboda ta saka hijibi, lamarin da ya fuskanci akkakusar daga kungiyoyin musumi da kuma na kare hakkin bil adama a ciki da wajen Amurka.
Robert Luna babban jami'in 'yan sanda a yankin ya bayyana cewa, a matsayinsu na jami'an tsaro suna kare dukaknin mutane ne ba tare da la'kari da banbancina ddininsu ko shigaru ta sutura ba, a kan haka dole ne su ma musulmi su samu wannan hakkin kamar sauran mutane a Amurka.
Majlalisar msuulmin Amurka ta ce tana jiran ta ga sauran jahohin kasar sun yi koyi da irin wannan mataki.
3558226