IQNA

23:47 - January 06, 2017
Lambar Labari: 3481107
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Morocco ta sanar da cewa za ta bayar da dama ga wasu bankunan kasar domin bude rassan bankin muslunci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani nay a habarat cewa ya nakalto daga shafin taqrib cewa, a jiya gwamnatin kasar Morocco ta sanar da amicewarta kan bayar da dama ga wasu bankunan kasar domin bude rassan bankin muslunci a kasar guda biyar.

Babbar manufar hakan ita ce kara farfado harkokin tattalin arzikin kasar da ya shiga cikin wani yanayi maras kyau, da kuma cika alkawalin da jamiyyar masu da'awar kishin Islama ta kasar ta yi wa mutane, kan cewa za ta bude rassa bnakin muslunci idan aka zabe ta, inda kuma yanzu ita ce ta kafa majalisar ministoci.

Tun a cikin shekara ta 2011 ce jam'iyyar ta amsu kishin islama ta yi al'ummar kasar wannan alakawali, kuma za a bayar damar ne ga wasu muhimamn bankuna na kasar da suka hada da people's bank wanda yake da alaka da masarautar kasar, sai kuma BMCE Africa.

Haka nan kuma CIH wanda shi ma yake da alaka da gwamnati wanda kuma yake bayar da rance ga manoma, zai samu damar bude wani reshe na bankin muslunci, inda hakan zai bayar da dama ga wasu cibiyoyin da suke da kudade a bankin su saka hannayen jaria Morocco.

3560079


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: