IQNA

Halin Rashin Tabbas A Bahrain Sakamakon Kisan Kai Da Masarautar Kasar Ta yi

23:45 - January 17, 2017
Lambar Labari: 3481142
Bangaren kasa da kasa, Tun bayan sanar da kisan matasa 3 'yan kasar Bahrain da masarautar kasar ta yi a ranar Lahadi da ta gabata, kasar ta shiga wani hali na rashin tabbas, inda ake ci gaba da gudanar da jerin gwano da zanga-zanga a dukkanin fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran kurani na IQNA ya habarta cewa, motsin al'ummar Bahrain na ci gaba tun daga 2011 domin neman hakkokinsu, a ci gaba da kisan kiyashin da ake yi wa al'ummar kasar tun daga wccan shekara, a safiyar Lahadin da ta gabata ce masarautar ta Bahrain ta sanar da cewa ta kashe Sami Mushaima, da Ali Abdulshahid Sankis da kuma Abbas Sami, kuma an kashe su ne ta hanyar harbi da bindiga, bisa zargin cewa suna da hannu a tayar da wani bam da ya kashe wani dan sandan hadaddiyar daular larabawa daga cikin jami'an tsaron da masarautar kasar ta dauka haya domin murkushe zanga-zangar da al'ummar kasar suka yi domin neman hakkokinsu da aka haramta musu, gami da wasu 'yan sanda biyu na kasar.

An danganta wannan tuhuma ga wadannan matasa ne ba tare da bayyana wa duniya wani dalili da ke iya tabbatar da abin da masarautar take tuhumarsu ba, kuma a lokacin da abin ya faru iyalansu da danginsu sun tabbatar da cewa dukkaninsu suna a wurare daban-daban suna hidimominsu na yau da kullum, to amma sakamakon matsin lambar da masarautar Bahrain ta fuskanta daga hadaddiyar daular larabawa, yasa ala tilas masarutar ta samo wani wanda za ta danganta wannan batu a kansa, domin kada tana nuna cewa ta gaza wajen kasa gano wadanda suka aikata laifin, inda wadannan matasa wadanda mabiya mazhabar shi'a ne da masarautar kasar ke adawa da su, suka zama ragunan layya a kan wannan lamari.

Iyalan wadannan matasa uku sun ce an ki mika musu gawawwakin 'ya'yansu domin su yi musu sutura kamar yadda addinin muslunci ya yi umarni, a maimakon hakan ma sai suka ji labarin cewa masarautar Bahrain ta bizne gawawwakin 'ya'yansu a wani wuri da ba a sani ba.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama da suka hada da na kasashen turai daga ciki kuwa har da Amnesty Int. da kuma Human Rights Watch, gami da wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasashen larabawa, duk sun yi tir da Allawadai da wannan kisa, yayin da wata babbar kungiyar lauyoyi a kasar Tunisia ta sha alwashin bin kadun wannan lamari tare da harhada bayanai domin gabatar da su ga kotun manyan laifuka ta duniya, domin kuwa a cewar wannan kungiya; an kashe wadannan matasa ba bisa ka'ida ta sahihiyar shari'a ko doka ba, domin kuwa an tuhume su da laifi, kuma sun musunta abin da aka tuhume su, an azabtar da su azabtarwa, har sai da aka tilasta su amsa laifin ba domin amincewarsu ba, domin inda ba su amsa da sun mutu saboda azabtarwar, an hana lauyoyi da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama na ciki da wajen kasar su ga wadannan matasa tun daga lokacin da aka kama su har zuwa lokacin da aka kashe su, wanda hakan ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na duniya, a kan haka wanann kungiya ta lauyoyi ta sha alwashin sai ta yi shari'a da masarautar Bahrain a kotun manyan laifka ta duniya bisa tuhumar wannan masarauta da laifin kisan kai na ganganci.

A bangaren cikin gida kuwa, kasar ta Bahrain wadda fiye da kashi 80% na al'ummarta mabiya mazhabar shi'a ne, tana ganin zanga-zanga mafi girma da bata taba ganin irinta a tarihi ba, yayin da malaman addini suka ce babu ruwansu da duk abin da zai biyo bayan kisan wadannan matasa 3, domin kuwa sun gargadi masarautar kasar da kada ta tafka wannan babban kure wanda za ta yi nadama a kansa a lokacin da nadama ba za ta yi amfani ba, amma duk da hakan ta aikata wannan kisan kai, wanda tabbas al'ummar kasar ba za su taba amincewa da hakan ba.

Yanzu haka dai kungiyar Wafa Al-islami, daya daga cikin manyan kungiyoyin addini a kasar, ta sanar da cewa za ta dauki makamai domin kare kanta daga zaluncin da kama karya na masarautar kasar, wanda ake ganin ga dukaknina alamu akwai wasu kungiyoyin da suke kan hanyar yin hakan, a daidai lokacin da masarautar Bahrain hatta 'yan sanda sai ta dauko haya daga wasu kasashen larabawa da Pakistan domin su bata kariya, wanda hakan ke nufin cewa kasar ta kama hanyar shiga wani sabon rikici da ba a san inda zai tsaya ba, domin kuwa masarautar kasar ba za ta iya taka wa fushin al'umma birki ba, duk kuwa da goyon baya da kariyar da take samu daga kasashen turai.

3563232


captcha