IQNA

23:48 - January 17, 2017
Lambar Labari: 3481143
Bangaren kasa da kasa, mataimakin gwamnan jahar bauchia tarayyar najeriya ya bayyana a wajen rufe gasar kur'ani cewa, karatun kur'ani mai tsarki wata baiwa daga Allah.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Daily Trust cewa, Nuhu Gidado mataimakin gwamnan jahar Bauchi ya ce karatun kur'ani mai tsarki wata baiwa ce daga Allah wadda ba kowane ke samun irinta ba.

Haka nan kuma ya yi godiya tare da jinjina wa matasan da suka samu damar halartar gasar kur'ani ta kasa ta shekarar 2017 da aka gudanar a jahar ta Bauchi, tare da bayar da kyautuka gare su, da kuma kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo.

Gasar da aka gudanar a jahar Bauchi ta hada makaranta maza da mata, kuma ta fara ne daga izihi na 2 zuwa izihi na 10, zuwa izihi na 20, sai kuma izihi na 40.

Gasar ta samu halartar makaranta daga jahohi ashirin daga cikin jahohi talatin da shida da kasar take da su gami da babban tarayya.

3563188


Abubuwan Da Ya Shafa: IQNA ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: