IQNA

22:43 - January 20, 2017
Lambar Labari: 3481152
Bangaren kasa da kasa, Magoya bayan harkar muslunci a Najeriya sun gudanar da jerin gwano a birane daban-daban na Najeriya domin neman a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya nakalto daga shafin alalam cewa, magoya bayan harkar musluncin sun gudanar da jerin gwano ne domin kiran gwamnati da ta saki jagoran harkar muslunci a kasar (Islamic Movement) Sheikh Ibrahim Zakzaky, bayan da wa'adin da kotun tarayya da ke Abuja ta bayar kan a sake shi a cikin 45 ba tare da wani sharadi ba.

Wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama a Najeriya da ma wasu na kasa da kasa, sun bi sahun magoya bayan harkar musulunci, wajen kiran gwamnatin tarayyar Najeriya da ta mutunta dokar kasa, ta hanyar aiwatar da umarnin kotun tarayya.

Duk kuwa da cewa a daya bangaren daga bisani bayan shudewar wasu kwanaki dakarewar wa’adin da kotu ta baiwa gwamnatin tarayya kan ta saki malamin, maimagana da yawun fadar shugaban kasar ya fito ya ce akwai dalilai da suka sanya ba za su saki sheikh Zakzaky ba, daga ciki kuwa har da tson kasa da kuma kiyae bukatun ‘yan kasa.

3564562


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: