Baya ga hakan kuma jami'an tsaron sun ce mutanen sun zauna a cikin masallaci fiye da mintuna goma bayan sallar Magariba, duk kuwa da cewa an kafa doka a kan musulmi kan su gaggauta ficewa daga cikin masallaci da zaran sun kammala sallar magariba, tare da hana su gudanar da sallar isha'i a cikin masallatai.
Makonni biyu da suka gabata ne ministocin harkokin wajen kasashen musulmi suka gudanar da zama a birnin Kualalampour na kasar Malayzia, inda suka tattauna kan halin da musulmin kasar Maynmar ke ciki, da kuma taimakon da za su iya ba su.