IQNA

Shirin Trump Na Mayar Da Ofishin Jakadancin Amurka Zuwa Quds Ya Dami Palastinawa

16:56 - February 01, 2017
Lambar Labari: 3481192
Bangaren kasa da kasa, Jakadan gwamnatin kwarya-kwaryan cin gishin kai ta Palastina a kungiyar hadin kan kasashen larabawa, ya gabatar da wani daftarin kudiri da ke neman kasashen larabawa da su taka wa shirin Trump birki, kan batun dauke ofishin jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa Quds.

Kamnin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran arabi daga birnin Alkahira na kasar Masar ya bayar da rahoton cewa, Jamal Shaubaki jakadan Palastinu a kungiyar hadin kan kasashen larabawa ya gabatar da bukatar gwanatin Palastinu, da ke yin kira ga larabawa da su dauki matakan ganin sun hana Donald Trump dauke ofishin jakadancin Amurka daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Quds.

A cikin daftarin kudirin da ya gabatar ga kungiyar a yammacin jiya, gwamnatin Palastinu ta bukaci larabawa da su hada kai da sauran kasashen musulmi domin ganin Donald Trump bai samu nasarar aiwatar da shirin nasa ba.

A lokacin da yake karin bayani a kan daftrin kudirin, Jamal Shaubaki ya bayyana cewa, dukkanin al'ummar Palastinu suna cikin zullumi, domin rashin sanin makomar lamarinsu bayan da Donald Trump ya hau kan kujerar shugabancin kasar Amurka, domin kuwa a cewarsa kalaman da ke fitowa daga bakin Trump ba su yin bushara ta alkhairi ga al'ummar palastinu.

3569364


captcha