IQNA

22:49 - February 04, 2017
Lambar Labari: 3481199
Bangaren kasa da kasa, Kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya fitar da wani rahoto da ke cewa nuni da cewa, ga dukkanin alamu jami'an tsaron gwamnatin Myanmar sun tafka laifukan yaki a kan musulmi 'yan kabilar Rohingya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Safaqna cewa, Wannan rahoto na kwamitin kare hakkin bil adama ya tabbatar da cewa, jami'an tsaron kasar Myanmar sun yi amfani da karfi a kan fararen hula musulmi 'yan kabilar Rohingya a yankin Rakhin da ke arewacin kasar.

Rahoton ya ce; jami'an tsaron sun tafka laifin kisa a kan fararen hula da dama da yin fyade da kuma kone gidaje da kaddarorinsu, wanda hakan yana a matsayin laifin yaki, wanda kotun manyan laifuka ta duniya ke yin hukuncin a kansa.

Kwamitin ya ce ya samu cikakkun bayanai daga mutane da dama da wannan lamari ya rutsa da su, bayan tura wani kwamiti karkashin inuwar majalisar dinkin duniya, wanda ya ziyarci kasar ta Myanmar da kuma kasashen da ke makwaftaka da ita, musamman kasar Bangaladesh, inda aka tsugunnar da 'yan gudun hijira na kabilar Rohingya fiye da dubu 66 da suka tsere daga yankunansu da ke arewacin Myanmar a farkon watan Oktoban shekarara ta 2016 da ta gabata, domin tsira da rayukansu.

Daga cikin wadanda kwamitin na majalisar dinkin duniya ya ji ta bakinsu, sun bayar da bayanai makamantan juna kan irin ayyukan kisan kiyashin da jami'an tsaron gwamnatin Myanmar suka aikata a kan musulmin 'yan kabilar Rohingya, yayin da kuma kimanin rabin wadanda aka ji ta bakinsu sun tabbatar da mutuwar wani ko wasu daga cikin danginsu, wanda hakan ke nuni da cewa babu wasu alkalumma takamaimai kan adadin mutanen da jami'an tsaron na Myanmar suka kashe.

Kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin ya kirayi dukkanin kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa a kan abin da yake faruwa a kan musulmin kasar Myanmar, tare da yin binciken gaggawa a kan gwamnatin kasar, domin daukar matakar matakan da suka dace a kanta na doka dangane da abin da ke faruwa na kisan kiyashi da jami'an tsaronta gami da 'yan addinin Boda da take mara wa baya suke yi kan musulmin Rohingya.

A cikin 'yan makaonnin da suka gabata ne dai kasar Malaysia ta kirayi wani zaman taro na kasashen musulmi a birnin Kualalampour dmin daukar matakai dangane da halin da musulmin suke ciki a Myanmar, an dai kammala taron ba tare da daukar wani mataki na ladabtarwa akan gwamnatin ta Myanmar ba, yayin da sauran kasashen yammacin turai da ke babatun kare hakkin bil adama suke ci gaba da yin gum da bakunansu kan wannan mummunar ta'asa ta kisan kare dangi da ake aikatawa kan musulmin Mayanmar.

Abin jira a gani dai yanzu shi ne irin matakin da kasashen duniya za su dauka a kan batu, bayan da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya fitar da wannan rahoto kan halin da musulmin na Myanmar ke ciki.

3570071


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: