IQNA

An Kashe Babban Sakataren Kungiyar Hizbullah Ta Kasar Iraki

23:17 - February 09, 2017
Lambar Labari: 3481215
Bangaren kasa da kasa, wasu ‘yan ta’adda sun sun be wutar bindiga a kan babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, shafin tashar alalam ya bayar da rahon cewa, wasu wadanda ba a san ko su wanene ba sun bude wutar bindiga a kan motar Basim Musawi baban sakataren kungiyar Hizbillah a Iraki, kuma a na take ya yi shahada.

‘Yan ta’addan sun habi Basim Musawi ne a daren jiya a lokacin da ya fito daga cikin motarsa a wani titi da cikin garin Basara a kudancin kasar Iraki, kuma mutanen sun tsere bayan harbinsa, yayin da wani mutm da suke tare ya samu raunuka.

Basim Musawi dai ya kasance daya daga cikin mutanen da suka kafa rundunar dakarun sa kai da ke taimaka sojojin Iraki wajen yaki da ‘yan ta’’addan wahabiyawa na ISIS a kasar Iraki, inda kungiyarsa ta Hizbullah a Iraki ta shiga cikin rundunar sa kai domin yaki da ‘yan ta’adda.

Har yanzu dai babu wata kungiyar da ta sanar da daukar nauyin aikata wannan ta’asa, amma dai ko shakka babu ‘yan ta’adda da kuma gwamnatocin larabawan da ke daukar nauyinsu da kuma iyayen gidansu turawa suna dakonsa domin daukar fansa a kansa.

3572693


captcha