IQNA

16:16 - February 24, 2017
Lambar Labari: 3481258
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra'ila ta ware kudi dalar Amurka miliyan 190 domin karfafa samuwar yahudawa a cikin birnin Quds da kewaye.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, kamfanin dillancin Anatoly ya bayar da rahoton cewa, ministan Isra'ila mai kula da sha'anin birnin Zaif Algin ya bayyana cewa, babbar manufar ware wadannan kudade it ace karfafa yawun bude da baki 'yan kasashen waje ke zuwa a birnin Quds, tare da karfafa shirin tabbatar da birnin na Quds a matsayin bababn birnin Isra'ila.

Wannan na daga cikin ayyukan da gwamnatin Isra'ila take aiwatarwa a kowane lokaci, inda take ware kudade domin tarbar yahudawa daga kasashen duniya da suke zuwa birnin Quds, da sunan ana tarbar baki daga kasashen ketare, daga nan ne kuma wasu Isra'ila ke gamsar da su domin su baro kasashensu su dawo Isra'ila da zama.

A cikin watan da ya gabata ma gwamnatin Isra'ila ta amince da wani shiri an gina wasu matsugunna yahuwada 800 a cikin yankunan Palastinawa da ke gabashin birnin na Quds, domin tsgunnar da yahudawan da suka yi hijira zuwa Isra'ila.

3577651


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: