IQNA

16:50 - February 26, 2017
Lambar Labari: 3481265
Bangaren kasa da kasa, mutanen birnin Ohama na kasar Amurka sun nua gamsuwa da wani shiri da cibiyar muslucni ta birnin ta shirya.

BKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin thepeninsulaqatar ya habarta cewa, cibiyar musulmin birnin na Ohama ta gabatar da wani shiri na wayar da kan jama'a dangane da addinin muslunci

Babban limamain masallacin birnin ya gabatar da jawabi a wajen wannan taro, inda ya ce bababr manufar taron ita ce yin bayani kan addinin muslunci da kuma abubuwan da yake koyar da dan adam a rayuwa.

Daga cikin irin abubuwan da malamain ya mayar da hankali a kansu har yadda muslucni yake bayar da muhimmanci ga batutuwa da suka shafi rayuwar jama'a ta zamantakewa, inda muslunci yake kallon kyautata ruwar zamnatakewa a cikin manyan ayyuka na wajibi.

Haka nan kuma a bin da ya shafi hakkoki na dan adam inda muslucni yake girmama mutuma matsayinsa na dan adam tare da kare masa dukaknin hakkokinsa, inda misalign hakan shi ne yadda yahudawa da kiristoci suka rayu tare da amnzon Allah, har sukan fifita su kawo kara a wurinsa ko kuma neman buktunsu, saboda sanin adadlcinsa da tausayinsa da kuma mutuncinsa.

Da dama daga cikin wadanda suka halarci taro daga cikin mabiya wasu addinai ba muslunci ba sun bukaci da a ci gaba da gudanar da irin wannan jawabi, domin kuwa hakan ya kara gamsar da su kan cewa muslunci addinin zaman lafiya ne ba ta'addanci ba.

3578330

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: