IQNA

23:18 - February 27, 2017
Lambar Labari: 3481266
Bangaren siyasa, an gudanar da zaman taron makoki na farko domin tunawa da shahadar Fatima Zahra (SA) a husainiyyar Imam Khomenei (RA) tare da halartar jagora.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a daren jiya ne aka fara gudanar da zaman farko na tunawa da zagayowar ranakun shahadar Sayyidah Fatima Zahara (SA) tare da halartar jagoran juyin Islama na Iran Ayatollah Sayyid Ali kahmenei (DZ) da kuma shugaban kasa da shugaban majalisar dokoki da kuma alkalin alkalai da sauran jami’ai, gami da mutanen gari, taron da ya gudana a Husainiyar Imam Khomeni (RA).

A wurin wannan taro dai Hojjatol Islam Siddighiya gabatar da jawabi kan matsayin Sayyidah Zahra (SA) da kuma madaukakin matsayin da take da shi gami da falalolinta, da kuma gudunmawar da ta bayar wajen karfafa addinin Allah madaukakin sarki a lokacin rayuwarta.

Haka nan kuma a wani bangaren jawabin nasa ya yi ishara da cewa, babban umarnin ahlul bait a kowane lokaci yana da alaka ne da tabbatar da adalci da bin umarnin Allah a cikin dukkanin lamrra na rayuwa, da kuma yin riko da koyarwar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

Bin tafarkin manzon Allah da sunnarsa ta gaskiya su ne mabudin dukkanin kofofin samun rabo na duniya da lahira.

3573248


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: