Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga Malaysian Digest cewa, nan da ‘yan makonni masu zuwa a za fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin Kulalampoir fadar mulkin kasar.
A wannan gas ace dai za a fitar da wadanda za su wakilci a bababr gasar kur’ani ta duniya da ake gudanarwa a kowace shekara a kasar.
Siti Shahira day ace daga cikin makaranta daga jami’ar muslunci ta birnin Kualalampoir da ta samu damar wucewa zuwa gasar sharen fagen da za a gudanar, kuma ta bayyana farin ciki maras misiltuwa kan wannan nasara da ta samu.
Ta ce tun kafin wannan lokacin tana halartar masallaci domin karatun kur’ani, duk kuwa da cewa ita tana karantun likitanci ne a bangaren liktan hakora, amma duk da haka wannan ba zai hana ta shiga wannan gasar kur’ani ba.
A kowace shekara dai kasar Malaysia na daukar nauyin bakuncin gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta duniya, inda a wannan shekara kasashe 96 ne za su halarci wannan gasa.