IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Kasa A Burnei

20:33 - March 09, 2017
Lambar Labari: 3481297
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya a Brakas babban birnin Burnei.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Burneo Bulletin cewa, tun a ranar Talata da ta gabata ce aka fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani ta kasa a Burnei.

Gasar na samun halartar manyan jami'an gwamnati da suka hada da ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar, da ma wasu daga cikin manyan mutane da kuma malamai.

Daya daga cikin fitattun makaranta kur'ani daga Indonesia Muhammad farid Muftah ya fara bude wurin da karatun kur'ani mai tsarki, kafin daga bisani a shiga cikin shirin.

Gasar dai ta hada bangarori daban-daban da suka shafi karatu da kuma harda, sai kuma sanin kaidojin karatu da hukuncinsa, kuma ana gudanar da gasa a kowane bangare daga cikin wadannan bangarori.

Za a ci gaba da fitar da wadanda suka samu maki a kowane bangare suna karawa da juna har zuwa ga mataki na karshe, inda za a gudanar da gasa a kowane bangare domin fitar da matsayi na daya da na biyu da kuma na uku.

Daga karshe za a bayar da kyautuka ga dukkanin wadanda suka halarci gasar, kamar yadda kuma za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo a gasar.

A kowace shekara dai akn gudanar da gasar kur'ani sau kimanin 30 a Burnei, domin karfafa jama'a kan karatun kur'ani mai tsarki.

3581984
Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha