Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran shafaqana ya bayar da rahoton cewa, Samira Al Halaiqa 'yar majalisar dokokin Palastinu ce da ke nuna rashina mincewa da zaluncin Isra'ila a kan al'ummar Palastinu, da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki da sojojin Isra'ila ke yi.
Rahoton ya ce da jijjifin safiyar yau sojojin Isra'ila sun kai samame a kan gidanta da ke garin Al-shuyukh da ke kusa da birnin Alkhalil, inda suka fitar da ita daga cikin iyalanta, kuma suka da ita wani wuri da ba a sani ba.
Yanzu haka dai 'yan majalisar dokokin Palastinu 10 suke tsare a hannun jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila, da suka hada har da dan majalisa guda daga kungiyar Fatah, da kuma wasu daga kungiyoyin hamas da Jabhat Sha'abiyyah.