IQNA

23:55 - March 15, 2017
Lambar Labari: 3481316
Bangaren kasa da kasa, a ci gaba da kai farmaki da ake yi kan masallatai da cibiyoyin muslunci a Amurka an kai hari kan wani masalalci a jahar Arizona.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yanar gizo na «tucson.com» ya bayar da rahoton cewa, an kai hari kan wani masallaci a cikin jahar Arizona a wani mataki na tsokana ga musulmi.

Wannan dai na daga cikin abubuwan da ake gani a halin yanzu a wasu daga yankunan kasar Amurka tun bayan da shugaban kasar mai ci yanzu ya lashe zaben da aka gudanar.

Babbar manufar masu nuna kyama ga muslucni ita ce tunzura sauran masu adawa da muslunci su ci gaba da kai hari kan kaddarori da masalatan muslmi, wanda kuma hakan shi ne babban burin shugaban kasar Amurka na yanzu da gwamnatinsa.

Jami’an tsaro dai sun ce sun shiga gudanar da bincke domin gano wadanda suke da hannu wajen kaddamar da wannan hari a kan masalalcin musulmi tare da kone shi kurmus.

Koa cikin makon da ya gabata an kai wani hari makancin wannan a kan wani masallacin, wanda shi ma a ak kone shi, kuma har yanzu ba kama kowa ba.

3584368
Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Arizona ، Amurka ، masallaci ، tsokana ، musulmi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: