IQNA

23:52 - March 31, 2017
Lambar Labari: 3481362
angaren kasa da kasa, Hajiya Ra'ifah Sammadi da aka fi sani Ummu Hussain wata tsohuwa mai shekaru 70 a kasar Jordan ta hardace kur'ani mai tsarki baki daya.

BKamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin alsaa.net cewa, Hajiya Ra'ifa Sammadi mai zama a kauyen Arbad a kasar Jordan ta samu nasarar hardae kur'ani mai tsarki ta hanyar saurare

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan tsihuwa wadda ba ta iya karatu ba, ta yi amfani kasusuwa na karatun kur'ani, wanda kuma ta hanyar sauarre ta hardace kur'ani baki daya a cikin shekaru uku da watanni hudu.

Tashar radiyon yarmuk wadda ke gabatar da shirin kur'ani ita ce ta bayar da rahoto dangane da kokain da wannan tsohuwa ta yi, inda a halin yanzu ta shiga cikin mutane da ake aklfahari da su a kasar da ba za a manta da su ba.

3586172

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: