IQNA

Firayi Ministan Canada Ya Yi Allawai Da Keta Alfarmar Alkur'ani

22:45 - April 02, 2017
Lambar Labari: 3481368
Bangaren kasa da kasa, firayi ministan kasar Canada Justin Trudeau ya yi Allawadai da kakkausar murya dangane da yaga kwafin al'ur'ani mai tsarki da aka yi a jami'ar Ontario da ke kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na Aljazeera net ya bayar da rahoton cewa, wasu daliban jami'ar Ontario a cikin fushi sun gudanar da gangami, domin nuna fushinsu da kuma rashin amincewarsu da matakin da hukumomin ilimi suka dauka a yankin Pil, na bayar da dama ga dalibai musulmi da su gudanar da sallar Juma'a a cikin makarantu.

Daliban masu gangami sun nuna rashin amincewa da wannan mataki, tare da rera taken nuna kin jinin musulmi, baya ga haka kuma suka yaga kwafin alkur'ani mai tsarki tare da watsa takardunsa a wurin.

A nasa bangaren firayi ministan kasar Canada Justin Trudeau, ya fito ya yi tir da Allawadai da kakkausar murya a kan wannan aiki na dabbanci, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taba amincewa da nuna kyama ga wani bangare na jama'a a kasar ba, saboda addininsu ko akidarsu, domin kuwa a cewarsa Canada kasa ce da kowa yake da 'yancin ya gudanar da addininsa daidai da fahimtarsa, kuma babu wani da yake da hakkin cin zarafinsa.

Yankin Pil dai na daya daga cikin yankunan kasar Canada da ke yawan muuslmi, inda aka kaddara dalibai musulmi da suke karatu a makarantu da cewa adadinsu ya haur dubu 150.

3586282

captcha