Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da taroa cibiyar mulsunci da ke Hamburg a kasar Jamus domin tunawa da ranar zagayowar haihuwar Imam Ali (AS).
Haka nan a birnin Stockholm fadar mlkin kasar Sweden an gudanar da tarukan tunawa da zagayowar wanann lokaci mai albarka.
Cibiyar musulunci ta Vienna da ke kasar Austria ita ma ta dauki nauyin shirya gudanar da tarukan maulidin Iamm Ali (AS) a daren na jiya.
A can birnin Helsinki na kasar Finland ma an gudanar da taro na tunawa da zagayowar lokacin haihuwar shugaban muminai Ali (AS) tare da halartar daruruwan mabiya mazhabar iyakan gidan manzo.
A yau kuma ana gudanar da wannan taro a cibiyar musulnci da ke birnin Landan na kasar Bitaniya, wanda zai fara daga misalign karfe 18:15 na yammacin yau.
A taron Hojj. Muhammad Saeed Bahmanpour zai gabatar da lacca, yayin da shi kuma Haj Behzad Maulae zai gabatar da bege ga haifafafen ka’abah.