Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin technicianonline cewa, daliban sun gudanar da wani shiri ne mai taken makon fadakarwa a kan musulmci.
Shirin nasu dai ya kunshi gabatar da jawabai da kuma amsa atambayoyin sauran dalibai da suke bukatar sanin wani abu dangane da addinin muslunci, kamar yadda kuma suka gudanar da salla a cikin jami'ar a bainar jama'a.
Babbar manufar wananns hiri dai ita ce wayar da kan sauran dalibai wadanda ba musulmi ba, dangane da muslunci da kuma abubuwan da yake kira zuwa gare su, maimakon dogaro da abubuwan batunci da ake fada a kowane lokaci a kan ddinin muslunci da musulmi, sakamakon ayyukan da wasu masu kiran kansu musulmi suke aikatawa.
A jami'oi da daman a Amurka dalibai musulmi suna yin iyakacin kokarinsu domin ganin sun isar da sakon wayar da kai ta hanyoyin da suka samu dama, sakamakon irin matsalolin da musulmi suke fuskanta ahalin yanzu a kasar Amurka, bayan da sabuwar gwamnati mai adawa da musulmi ta hau mulki.
Bayan kammala sallar, an yi wa wasu daga cikin daliban jami'ar bayani a kan salla, da kuma abubuwan da musulmi suke karanta da kuma abin suke fadi a cikin ruku'u da sujada, wanda babu wai abu na aibu da ke ciki.