Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na akhbarona.com cewa, a yau ne aka fara gudanar da zaman taron, wanda zai yi dubi a akan muhimman lamurra da suka shafi ilmomi da kuma matsayinsu a cikin kur’ani.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro wanda shi ne irinsa na hudu da ake gudanarwa a kasar a kowace shekara, yana samun halartar masana da kuma malamai da masu bincike daga cikin kasar ta Morocco da kuma kasashen musulmi daban-daban.
Daga cikin muhimman abubuwan da taron zai yi dubia akansu, akwai ilmin kur’ani da kuma hadisi gami da tafsiri, bayan nan kuma akwai sauran ilmomi da suka shafi sanin zamantakewar al’umma, da sanin yanayin rayuwar jama’a, da nazarin halayyar dan adama da sauransu.
Dukkanin wadannan ilmomi da ma wasu ilmomin na daban, duk kur’ani mai tsarki yay i tsokacia kansu, wasu kai tsaye, wasu kuma ta siyakin ayoyin ko kuma bayanin wani lamari na daban.
Malamai da masana za su gabatar da laccoci da kuma makaloli da suka rubuta a fagage na ilimin kur’ani mai tsarki, kamar yadda wasu makalolin da suka shafi wasu ilmomin da suka danci kur’ani su ma za a gabatar da su domin karawa juna sani.