Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na lomazoma.com cewa, wannan shiri zai kebanci kananan yara ne zalla.
Wanann shiri wata cibiya ce da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a kasar ta Morocco ta bullo da shi, tare da mika shi ga ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar domin yin bahasi a kansa.
Daga karshe dai an amince da shirin, wanda zai fara nan da 'yan watanni masu zuwa, yanzu haka kuma an fara rijistar sunayen yara da za su shiga shirin, wadanda za a duba ko sun cika sharuddan da ake bukata kafin a dauke su.
Daga cikin abubuwan da shirin zai mayar da hankali a kansu dai har da koyar da yaran tafsirin kur'ani da ma'anarsa, da kuma yadda za su iya iar da sakon kur'ani ta hanyoyi na bayanin manoninsu.
Baya ga hakan kuma za a koyar da wasu daga cikin cikin ilmomi da suka danganci kur'ani da kuma hadisi, da ma ilmomin sanin zamantakewa da kyawawan dabiu da dai sauransu, bayan nan kuma yana da cikin abubuwan da shirin zai kunsa ta fuskar kira'a.
Babbar manufar shirin dai ita ce samar da hanyoyi na koyar da yara kur'ani mai tsarki, ta yadda hakan zai ba su damar hawa kan turbar zama malana kur'ani.