IQNA

Barazanar Kashe Limamin Masallacin A Kasar Canada

23:28 - April 20, 2017
Lambar Labari: 3481424
Bangaren kasa da kasa, wasu mutane da ba a san ko su wane nen ba sun yi barazanar kashe wani limamamin masalacin Juma'a a birnin Toronto na kasar Canada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da yake zantawa da kafar yada labarai ta Globl News, sheikh Ibrahim Hindi ya bayyana cewa, a jiya Laraba an kawo masa wani sakon wasika, wanda bayan buda sakon ya ga ana yi masa barazana da cewa ya shiga taitayinsa, domin kuwa akwai yiwuwar za a kashe shi.

Ya ce bai san mutanen da suka kawo wasikar suka saka cikin akwaitin wasiku da ke a kofar gidansa ba, amma a cewarsa yana ganin hakan ba zai rasa nasaba da kokarin da ya yi ba, na ganin an bayar da dama ga daliban jami'a a wasu yankuna domin su rika gudanar da sallar Juma'a a cikin jami'oinsu, wanda kuma wasu jami'oin sun amince da hakan, lamarin da ya fusata masu kiyayya da muslunci a kasar matuka.

3591560

captcha