IQNA

Na Yi Farin Cikin Samun Matsayi Na Biyu A Gasar Kur’ani

23:42 - April 29, 2017
Lambar Labari: 3481449
Bangaren kasa da kasa, Aiden Sharezad bdulrahman dan kasar Amurka ne da ya zo na biyu a gasar karatun kur’ani mai tsarki ta duniya a bangaren dalibai.

Aiden Sharezad Abdulrahman dan shekaru 15 da haihuwa, ya kasance daya daga cikin wadanda suka nuna kwazo matuka a gasar kur’ani mai tsarki ta duniya da aka gudanar a bangaren dalibai, inda ya samu nasarar zuwa amtsayi na biyu a gasar.

A lokacin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya bayyana cewa, hakika ya yi farin ciki maras misilltuwa da samun wanann babbar nasara a rayuwarsa, kuma dukkanin kokarin da ya yi bai tafi haka nan ba.

Wannan dalibi dai ya zo ne daga kasar Amurka, kuma ya kasance a cikin gasar ne a bangaren hardar dukkanin kur’ani mai tsarki, wanda kuma ya taka gagarumar rawa wajen gabatr da harda a lokacin gasar a cikin tsari mai ban shawa’awa.

Ya ci gaba da cewa tun yana dan shekaru 8 da haihuwa ya fara yin hardar kur’ani mai tsarki, kuma ya kammala hardar dukkanin kur’ani a cikin shekaru uku a lokacin da yake da shekaro 10 da haihuwa kenan a duniya.

Ya yaba matuka da irin tarbar da suka samu a Iran a lokacin wannan gasa, da kuma irin karamcin da ya ce an nuna musu maras misiltuwa, duk kuwa da cewa wannan bas hi ne karon farko da ya halarci irin wannan gas aba, domin kuwa ya je wasu kasashen da dama.

Daga cikin da ya ce ya je har da hadaddiyar daular larabawa da kuma Kuwait, kamar yadda kuma akasar Amurka a duk lokacinda ake gudanar da gasar kur’ani shi ne ke zuwa a matsayi na daya.


Matsayi Na Uku: Ina Bin Salon "Siddiq Minshawi” A Karatuna

"Albashir Abubakar” sdaga jamhuriyyar Nijar shi ne ya zo a matsayi na uku a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a bangaren dalibai kuma abangaren hardar kur’ani mai tsarki.

A zantawarsa da kamfanin dillancion labaran IQNA ya bayyana cewa, ya yi farin ciki matuka da samun matsayi na uku a wannan gasa ta duniya wadda aka gudanar a karo na biyar a bangaren dalibai a jamhuriyar muslunci.

Ya ci gaba da cewa, ya fara hardar kur’ani tun yana dan shekaru 4 da haihuwa, kuma ya hardace kur’ani baki daya a lokacin da yake da shekaru 10 a duniya.

Kuma a cewarsa mhaifansa sun taimaka masa matuka wajen ganin ya samu karatun kur’ani mai tsarki, kuma dukkanin karatun nasa ya yi a cikin gida ne har ya kammala hardarsa.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, yana bin salon karatun Siddiq Minshawi ne a cikin karatunsa, kasantuwar yana jin dadin salon da wannan malami yake amfani da shi a wajen karatun kur’ani mai tsarki.

3593979


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha