IQNA

Jagoran Juyin Islama:

‘Yan Takara Dole Ne Su Bayar Da Muhimmanci Ga Taimaka Ma Marassa Karfi

23:02 - May 01, 2017
Lambar Labari: 3481454
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya bayyana cewa dole ne dukkanin ‘yan takarar shugabancin kasa su mayar da hankalia kan bangaren jama’a marassa karfi idan sun samu nasara a zabe, domin tabbatar da cewa dukkanin al’umma sun samu adalcia cikin dukkanin lamarran gudanarwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei yayin ganawarsa da dubun dubatan Ma'aikata a jiya Lahadi yayi ishara kan zabe mai zuwa, tare kuma da yin galgadi ga 'yan takarar Shugabancin kasar shida kan su himmatu wajen tunani kan abinda zai gyara Al'ummar kasar, sannan kuma ya bukaci Al'ummar kasar da su fito kwansu da kwalkwatar su domin kada kuri'insu.

A yayin da ya rage kasa da kwanaki 20 a gudanar da zaben Shugaban kasa da na kananen hukumomi,Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar fitowar al'ummar Iran kwansu da kwarkwatarsu yayin zabe a koda yaushe yana rage irin makircin makiya a kan su, don haka ya kirayi al'umma da su fito kwansu da kwarkwatarsu yayin zabe mai zuwa wanda shi ma zai rage sharrin makiyan a kansu.

Ayatullah Khamenei, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi a jiya Lahadi da dubun dubatan ma'aikatan kasar Iran a daidai lokacin da ake shirin gudanar da bikin ranar ma'aikata ta kasa inda ya ce : Batun fitowar mutane yayin zabe wani lamari ne mai matukar muhimmanci da zai kara tabbatar da tsaron kasa, don kuwa matukar mutane suka fito to kuwa Iran za ta ci gaba da zama cikin tsaro da kwanciyar hankali.

Zabe wani bangare ne mai mahimanci a kasashen dake kalkashin tsarin tafarkin Demokaradiya,kuma wannan bangare a kasar Iran Iran na gudana ne bisa tsarin musulinci da kuma mutunta ra'ayin Al'ummar kasar, jagoranci da kuma bukatun Mutane nada matsayi na musaman wanda kuma idan aka kwatamta tsarin zaben Iran da na wasu kasashe,mahimancinsa zai bayyana da cewa Al'umma a Jumhoriyar musulinci ta Iran su ke da maganar farko da ta karshe a yayin zabe, kuma suke zaben 'yan takarar da ya fi cancanta bayan da Majalisar tattance 'yan takara ta kamala zaben wadanda suka caccanci tsayawa takara daga cikin Mutanan da suka yin rajistar tsayawa takara, suka bashi amanarsu na jagorancin kasar.

Misali a kasar Amurka dan takarar da ya fi samun ra'ayin Mazabu shi ne ke zama Shugaban kasa, ba wai wanda ya fi yawan kuri'u ba domin hakan ra'ayin Al'umma bai yi tasiri sosai ba kamar yadda ya kamata.

Haka nan yayin da yake magana kan 'yan takaran da ya kamata a zaba, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar ba zai ce ga wanda za a zaba ba, sai dai ya ce yana kiran al'umma da su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi duk wanda suka ga ya dace. Jagoran ya ci gaba da cewa: Tsoron kasantuwar mutane a fage shi ne babban dalilin da ya sanya makiya suke tsoron wuce gona da iri a kan Iran.

Jagoran yayi watsi da ikirarin da wasu suke yi na cewa shigowarsu fagen siyasa a matsayin dalilin da ya kawar da hatsarin yaki a kan Iran inda ya ce hakan kuskure ne don kuwa kasantuwar mutane a fage shi ne ya kawar da hatsarin yaki da wuce gona da iri a kan Iran.

A ranar 19 ga watan Mayun nan ne za a gudanar da zaben shugaban kasar ta Iran inda aka kiyasta cewa kimanin mutane miliyan 55 ne suka cancanci kada kuri'unsu inda za su zabi daya daga cikin 'yan takara 6 da suka tsaya ciki har da shugaba mai ci yanzu.

3594535


captcha