Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na asianews.network cewa, Federica Mogherini babbar jami’a mai kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar trai ta bayyana cewa, gudanar da bincike kan zargin kisan musulmi ‘yan kabilar Rohingya a Myanmar zai taimaka matuka wajen gano hakikanin abin da yake faruwa.
Mogherini ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da ministan harkokin wajen kasar Myanmar Ang San Suchi, inda ta ce bisa la’akari da kudirin da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya fitar kana bin da yake faruwa a Myanmar, gudanar da sahihin bincike ne zai iya bayar da damar tantance hakikanin abin da yake faruwa.
Sai dai a nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar ta Myanmar ya bayyana cewa, ba su gamsu da rahoton da kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suke bayarwa kan rikicin kasar ta Myanmar ba, wanda kuma a kan haka ne kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar duniya ya fitar da kudirinsa.
A watanni baya ne kwamitin kare hakkin bil adama ya fitar da wani kudiri, wanda ya yi Allawadai da kisan musulmin kasar Myanmar ‘yan kabilar Rohingya, tare da dora alhakin hakan a kan sojojin gwamnatin kasar, da kuma ‘yan addinin buda masu tsatsauran ra’ayi.