IQNA

Kur'ani Mafi Tsawo A Duniya Ana Gab Da Kammala Aikinsa

11:55 - May 05, 2017
Lambar Labari: 3481483
Bangaren kasa da kasa, Sa'ad Muhammad wani kwararren mai fasahar rubutu ne wanda a halin yanzu yake rubuta kur'ani mai tsawo domin ya zaman a daya a duniya.

Kamfanin dilalncin labaran iqn aya nakalto daga kamfanin dillancin labarai na shafaqna cewa, Muhammad sa'd tun yana karamin yaro ya dakatar da karatu a makaranta, inda ya shagaltu da koyon fasahar rubutun larabci.

A halin yanzu yana rubuta wani kwafin kur'ani mai tsarki da salon rubutu na fasaha, wanda kuma tsawonsa zai kai mita 700 idan aka kammala aikinsa, wanda kuma zai zama shi ne kur'ani mai fi tsawo a tarihin duniya.

Ya ce babbar manufar yin hakan ita ce gubatar da wani aiki na musamman a cikin addinin muslunci wand aba taba yin irinsa ba, domin kuwa kur'ani mai tsarki shi ne littafi mafi muhimamnci a rayuwar musulmi, a kan ya sha alwashin yin wani aiki na musamman ga kur'ani wanda zai ja hankulan al'ummomin duniya zuwa ga wannan littafi mai tsarki.

A zantawarsa da kamfanin dillanin labaran Reauters ya bayyana cewa; shi ne da kansa yake samun kudin da yake daukar nauyin wannan aiki da yake gudanarwa, na rubuta kur'ani mai tsawon mita 700, wanda an dauki shekaru uku ana gudanar da shi, kuma ana gab da kammala shi.

3596157
Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha