Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai Sada cewa, an kaddamar da wannan kamfe ne a mataki na kasa da kasa, da hakan ya hada yankunan palastinawa da kuma sauran kasashe da wannan kungiya take da wakilai, da suka hada da kasashen larabawa da kuma wasu kasashen Asia da naturai da kuma Afirka.
Babban manufar wannan kamfe dai ita ce sanar da al’ummomin duniya halin da ake ciki a birnin Quds, da kuma irin keta alfarma da wurare masu tsarki na musulmi da kuma kiristoci suke fuskanta daga yahudawan Isra’ila, da hakan ya hada da masallacin Quds mai alfarma.
Daga cikin ayukan da kungiyar za ta mayar a gaba har da nuna hotuna da kuma fina-finai kan yadda yahudawa suke cin zarafin jama’a da kuma yi musu kisan gilla a birnin Quds da kuma sauran yankunan palastinu, gami da yadda suke keta alfarmar masallacin Quds da sauran wurare masu tsarki da ke birnin.