Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga tashar PressTV cewa, dakarun masarautar ‘ya’yan Saud sun yi dirar mikiya da manyan makamai da motoci masu sulke a kan gidan jama’a fararen hula a cikin garin Awamiyya, inda suka yi ta harbe-harbe, tare da kasha farar hula hula guda da kuma jikkata wasu da dama.
Babu wani dalili da masarautar ta bayar kan wannan aikin zalunci, amma kuma wannan bas hi ne karon farko da al’ummar wannan yanki suke ganin cin zarafi da torarci daga mahukuntan masarautar ‘ya’yan gidan saud ba, domin kuwa yanki ne na mabiya mazhabar ahlul bait (AS) wadanda su ne kashi 15 cikin dari na dukkanin al’ummar kasar.
Yankin Qatif da ke gabashin Saudiyya, yanki ne na mabiya mazhabar shi’a, wanda kuma daga nan kasar take fitar da dukkanin azrkin danyen mai da isgar gas da ta dogara da shi.
Al’ummar wannan yanki dai suna kokawa a kan yadda ake fitar da arziki daga yankinsu amma kuma su ne aka fi haramta amfana da shi, bil hasali ma ana mayar da su saniyar ware a cikin dukkanin lamurran kasar a matsayinsu na ‘yan kasa saboda banbancin mazhaba, wanda kuma a kan haka ne masarautar kasar ta kasha babban malami daga yankin wato sheikh Nimr a shekarar da ta gabata.