IQNA

Aikin Gyaran Masallacin Laka Mafi Girma A Duniya Da Ke Mali

23:15 - May 12, 2017
Lambar Labari: 3481506
Bangaren kasa da kasa, jiya ne daruruwan mutane suka gudanar da aikin gyaran masallacin garin Djenné da ke kasar Mali, masallacin ginin Laka zalla mafi girma a duniya.
Aikin Gyaran Masallacin Laka Mafi Girma A Duniya Da Ke Mali

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na Dunya Bultin ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da aikin gyaran masallacin Djenne kamar yadda aka saba yi a kowace shekara, inda jama'a kan aikin a tare, yayin da magina kuma sukan dauki nauyin yin aikin gini yabe a kan bangayen masallacin, al'ummar Mali na gudanar da wannan aiki ne a rana ta musamman da suke kira idin laka.

Wannan masallaci dai shi ne masallacin da aka gina da laka zalla mafi girma a duniya, an kuma gina masallacin tun a cikin karni na 13, kimanin shekaru dari takwas da suka gabata.

Hukumar raya al'adu da kiyaye wurare da kayan tarihi ta duniya UNESCO, ta sanya wannan masallaci a cikin muhimman wurare na tarihi a duniya.

3598140

Aikin Gyaran Masallacin Laka Mafi Girma A Duniya Da Ke Mali

Aikin Gyaran Masallacin Laka Mafi Girma A Duniya Da Ke Mali

Aikin Gyaran Masallacin Laka Mafi Girma A Duniya Da Ke Mali
captcha