Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Bahram Qasimi a cikin daren jiya Juma'a ya fitar da sakon ta'aziya da alhini kan harin ta'addancin da aka kai kan tawagar jami'an gwamnatin Pakistan a lardin Boulochistan da ke kusa da kan iyaka da kasar Iran, yana mai bayyana cewa bunkasar ayyukan ta'addanci da tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya da Asiya wani mummunan makirci ne da marassa ruhin dan Adamtaka sukakitsa domin cimma munanan manufofinsu musamman a kan kasashen musulmi.
Qasimi ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba da jaddada cewa; Dole ne a dauki tsauraran matakan murkushe kungiyoyin 'yan ta'adda daga tushensu ta hanyar samun hadin kai da taimakekkeniya a tsakanin kasashen duniya.
A jiya ce bayan kammala sallar Juma'a aka kai harin bom a kan hanyar shigewar tawagar mataimakin shugaban Majalisar Dattijan kasar Pakistan Maulana Abdul-Ghaffar Haidari a garin Mastung da ke kudancin lardin Boulochistan na kasar, inda harin ya lashe rayukan mutane akalla 25 tare da jikkatan wasu 37 na daban, amma mataimakin shugaban Majalisar Dattijan ya tsira da ransa, sai dai harin ya raunata shi kadan, kuma kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta dauki alhakin kai harin.