Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Pak Obsever cewa, a jiya ne matar shugaban kasar Pakistan ta jagoranci bude wani taron kur'ani a cikin jami'ar Islam abad fadar mulkin kasar.
A lokacin da take gabar da jawabi ta bayyana cewa, kur'ani mai tsarki ta babbar da cewa, sha'anin kur'ani mai tsarki babbar ni'ima ce ga dukaknin msuulmi, domin kuwa a duk lokacin da aka samu musulmi suna karatu kuma suna hardar kur'ani, hakika za su gaba ci gaba a dukkanin bangarorin rayuwarsu.
Begam Mahmude ta ce daya daga cikin abubuwan da suka jawo wa musulmi matsaloli a cikin kasashensu har yin watsi da koyarwar kur'ani mai tsarki wadda manzon Allah (SAW) ya koyar da musulmi kamar yadda Allah ya umarce shi.
Daga karshe ta ce za su ci gaba da kara bayar da himma wajen kayutata lamarin kur'ani a kasar, tare da tabbatar da cewa matasa musamman masu tasowa sun amfana da shirye-shirye na kur'ani a kasar.