Ofishin kula da harkokin al’adu na kasar Iran a Tanzania ya sheda wa kamfanin dillancin labaran iqna cewa, an fara gudanar da taron shekara-shekara da ake gudanarwa na karatun kur’ani tare da tafsirinsa.
An bude wannan taron ne tare da halartar Iraniyawa mzauna birnin Darssalam na kasar Tanzania tare da wasu ‘yan kasar.
Haka nan kuma an fara ne da gabatar da jawabi wanda Hojjatol Islam Bagheri ya gabatar, daga nan kuma sai shugaban jami’ar Almustafa a kasar ta Tanzania Sayyid Hussain razavi, wanda shi ma ya gabatar da jawabi ga mahalarta wanann taro.
Babban abin da bayanin malaman biyu yafi mayar da hankali a kansa shi ne mayar da hankali wajen aikin ibada a cikin wannan wata na Ramadan mai alfarma, tare da kiyaye abubuwan da Allah madaukakin sarki ya haramta ga bayinsa.
Babban abin da aka fi son a mayar da hankali gare shia cikin watan Ramadan shi ne karatun kur’ani mai tsarki, wanda ake ninka ladarsa ninkin ba ninki.
Ana gudanar da wannan karatu ne juzu’iibiyu a kowace rana, bayan an kammala karatu sai kuma a yi bayai a kan wasu daga cikin ayoyin da aka karata, da kuma irin darussan da suke koyar da mutane.
Haka za a ci gaba da yi har zuwa karshen watan Ramadan mai alfarma, wanda kuma ofishin yada al’adun muslunci na Iran ne a kasar ta Tanzania zai ci gaba da daukar nauyin taron karatun.