Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na QAF cewa, Anwar Alhasnawi shugabar bangaren mata a kana bin da ya shafi kur’amni a karkashin cibiyar kur’ani ta hubbaren Alawi ita ce ta jagoranci wannan gasa.
Ta bayyana cewa, babbar manufar gudanar da wannan gasa ita ce yada koyarwar al’kur’ani mai tsarki, a kan haka ne a ka zabi wannan lokaci da ake gudanar da ibadar azukimia cikin wannan wata mai alfarma domin gudanar da wannan gasa ta kur’ani.
Gasar dai an gudanar da ita ne a rubuce, inda aka bayar da tambayoyi da suka danganci wasu lamurra da suka shafi kur’ani, da kuma Karin haske kan wasu abubuwan da kur’ani ya ambata a cikin wasu ayoyi, bayan na kuma an gudanar da gasar a bangaren nahjul balagha.
Ta ce an tanaji wasu kyautuka na musamman da za a bayar ga wadanda suka nuna kwazoa gasar, wanda kuma za a basu ne a lokacin gudanar da taron rufe gasar.