IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Kasar Jibouti

23:56 - June 05, 2017
Lambar Labari: 3481584
Bnagaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasar Jibouti.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an fara gudanar da wata gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Jiboutia kowace shekara, tare da halartar makaranta daga Somalia, Sudan, Uganda, Aljeriya, Yemen, Kenya Tanzaniya da kuma Komoros.

Wannan gasa dai an fara gudamar da ita tun bayan da shugaban kasar Isama'il Umar Gileh ya kafa ma'aikatar kula da harokin addinai a kasar Jiboutia cikins hekara ta 1999.

Shugaban kasar ya bayar da uuamnin gudanar da gasar kur'ani ta kasa da kasa a kowace shekara, inda akan samu halartar baki daga kasashen Afirka da suka gudanar da karatu da kuma harda.

Daga karshen gasar dai bisa al'ada shugaban kasar yana bayar da kyautua na musamman ga wada suka nuna kwazoa bangarorin da aka gudanar da gasar, wanda hada da hardar izihi 20 da kuma hardar izihi 10, baya ga karatun kur'ani mai tsarki.

3606520


captcha